Muna zaune ne a cikin ɗaya daga matsattsun gidajen da ke rukunin gidaje mai hawan bene da yawa wanda ke matsayin wurin zama ga iyalai masu matsakaicin samu da dama. Sai dai kuma, iyalin Kyanwar Gida da suka tare a rukunin gidajen yawansu zai iya ninka na mutanen da ke rayuwa a ciki. Saboda waɗannan dabbobi masu lanƙwasassun farata, waɗanda za su iya kama da iyalan dabbobi irin su – Zakuna, da dangogin Damisa daban-daban ba sa tsoron kowa a farfajiyarmu. Ƙaruwar yawan kyanwoyi masu farata tara a yatsunsu abu ne da ya dami kowane mutum inda kuma ya kasance abin raha da mutane masu yawa.
Waɗannan kyanwoyi da ke layinmu suna da wani tsari na yankin mallaka in da babu wanda ke shiga na wani. Gidan ƙasa, hawa na farko da na biyu na masu farautar beraye ne kuma ba sa barin yankunansu sai dai na ‘yan lokutan da sukan ƙetare iyaka su shiga ɗakunan girki. Baranda kuwa musamman ta ƙanana ce inda kuma lokaci zuwa lokaci manya daga dangin kyanwoyi na Siam suke amfani da shi don lasar jiki da shan hantsi. Wasu daga cikin mazajen kan sami lafiyayyun lungunan su yi ta sharar barci a wuraren da babu sararin jawo kyanwa ciki, kamar ɗakin maigadi, inda za su iya tarar da bawan Allan yana jan minshari. Allah ya yi wa waɗannan kyanwoyi da salon murya iri biyu ɗaya don yi gurnani ɗayan kuma don yin kuka da shi saboda haka wasu ‘yan tsiraru daga mawaƙan kyanwoyin da ke yankinmu su ke hana gabaɗayan mazauna wurin barci da tarukansu na dare a wasu lokuta na musamman.
Wasu daga mazauna rukunin gidajen waɗanda ke son zama fes fes a siga kamar kyanwa su kan ji haushi yayin da waɗannan toka-tokar kyanwoyi suka yamutsa musu kaya. Masu zafin rai cikin mazauna wurin suna ganin ba makawa sai an yi waje da waɗannan kyanwoyi da bulala mai baki tara. Amma ‘yan a-zauna-lafiya ba su yanke hukunci ba tukuna suna jiran su ga ta inda kyanwa za ta ɓullo. To, sai dai ba mu sani ba ko waye zai tari aradu da ka!